BBC navigation

An bankado cuwa-cuwar man fetur a Najeriya

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:35 GMT

Wani sabon rahoto akan yadda ake tafiyar da harkokin man fetur da iskar gas a Najeriya ya bankado yadda kasar ke asarar biliyoyin daloli a kowace shekara sakamakon badakalar da ake yi a wannan sashen.

Gwamnatin Najeriyar ce dai ta kafa kwamitin da ya gudanar da binciken wanda tsohon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzukin kasar ta'annati, Malam Nuhu Ribado, ya jagoranta.

Rahoton ya gano yadda abubuwa suka tabarbare a harkar man da gas na Najeriya.

Kwamitin yace a cikin shekaru goma da suka wuce an yi asarar kimanin dala bilyan 29 wajen cuwa-cuwa a fannin.

Ya kuma ce kasar na bin kamfanonin mai fiye da dala bilyan ukku na harajin hako man da ya kamata su biyata.

Kwamitin kuma ya yi batun satar danyen man fetur, wanda ya ce ana sace kusan kashi goma bisa 100 na man da kasar ke hakowa -- wanda aka kiyasta kudinsa akan dala bilyan shidda a kowace shekara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.