BBC navigation

Ma'aikatan hakar ma'adanai a Afurka ta Kudu sun koka

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:16 GMT
Ma'aikatan hakar ma'adanai a Afirka ta Kudu

Ma'aikatan hakar ma'adanai a Afirka ta Kudu

Kamfanin hako zinare da yafi kowanne girma a Afrika ta Kudu, AngloGold Ashanti ya bi sawun wasu kamfanonin kasar na korar dubban ma'aikatansa saboda shiga yaajin aiki.

Kamfanin ya ce, ya soma yinkurin sallamar ma'aikantansa dubu 12, wato daya bisa uku na adadin yawan ma'aikatansa a Afrika ta Kudu baki daya.

AngloGold Ashanti ya kara da cewar ya soma tattaunawa da wasu kungiyoyin kwadago kuma yana saran cewar za su sasanta nan bada jimawa ba.

A ranar Talata ma, daya daga cikin kamfanoni mafi girma a Afrika ta Kudu, wato Gold Fields ya sanarda korar ma'aikatansa fiye da dubu takwas.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.