BBC navigation

Wuta ta mamaye masana'antar makamai a Sudan

An sabunta: 24 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:48 GMT
Masana'antar hada makamai a Khartoum babban birnin kasar Sudan

Masana'antar hada makamai a Khartoum babban birnin kasar Sudan

Wata gagarumar wuta ta mamaye masana'antar hada makamai a Khartuom babban birnin kasar Sudan, bayan wata fashewa mai karar gaske da aka ji.

Sannan an kara jin wasu fashe-fashen a lokacin da 'yan kwana-kwana suke kokarin kashe wutar a masana'antar ta Yarmouk.

An ruwaito gwamnan jihar Abdul Rahman Al-Khider Rahman yana cewa an garzaya da wasu mutane asibiti bayan da suka shaki hayaki kuma in ban da su babu wasu da suka jikkata a sanadiyyar fashewar.

Haka kuma ya ce yana ganin fashewar ta farko da ta haddasa wutar ta auku ne a wani daki na ajiya dake masana'antar kuma ana gudanar da bincike akan abin da ya haddasa fashewar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.