BBC navigation

"Afirka za ta iya ciyar da kanta, amma..."

An sabunta: 25 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:50 GMT
Masu fama da matsalar yunwa a sansanin Dadaab, Kenya

Mutane fiye da miliyan ashirin ne ke fama da matsalar yunwa a Afirka

Bankin Duniya ya bayyana cewa nahiyar Afirka za ta iya ciyar da al'ummarta idan aka takaita tsauraran ka'idojin cinikayya tsakanin kasashe.

A cewar Bankin, kashi biyar cikin dari ne kacal na hatsin da kasashen Afirka ke saye yake fitowa daga sauran kasashen nahiyar.

Bankin ya kara da cewa janye ka'idojin zai taimaka wajen habaka cinikayya a tsakanin kasashen, ya rage farashi, sannan ya samarwa gwamnatoci kudin shiga na biliyoyin daloli.

Rahoton ya kuma kiyasta cewa kusan mutane miliyan ashirin ne ke fama da yunwa a yankin Sahel na Yammacin Afirka.

A cewar mataimakin shugaban Bankin na Duniya mai kula da Afirka, Mukhtar Diop, "Sau da yawa iyakokin kasashe kan hana abinci kaiwa ga gidaje da al'ummun da ke cikin yanayin hannu-baka-hannu-kwarya".


Tsauraran ka'idojin cinikayya kan kuma sanya farashin kayayyakin abinci ya tashi, sannan ya rage karsashin manoma na samar da abinci, tun da abin da ke kaiwa hannunsu bai taka kara ya karya ba.

Kudin mota na jawo hauhawar farashi

Tsadar kudin mota, ciki har da na-goron da a kan bayar a wuraren duba ababen hawa da wanda ake baiwa jami'an tsaron kan iyaka, da ma tsauraran ka'idojin da ke takaita amfani da ingantaccen irin shuka da takin zamani kan sanya al'amarin ya kara tabarbarewa, inji Bankin na Duniya.

A cewar wani jami'in Bankin, Paul Brenton, "Kalubalen da ake fuskanta shi ne yadda za a samar da wani yanayi inda gwamnatoci za su rungumi manufofi na-gari wadanda za su karfafa gwiwar masu zuba jari da 'yan kasuwa don su taimaka a bunkasa harkar noma a nahiyar".

Bayan farin da aka samu a kasashe da dama, farashin kayayyakin abinci na ta hauhawa a fadin duniya, ya kuma kusa kaiwa matakin da ba a taba ganin kamarsa ba tun shekarar 2008, shekarar da farashin ya yi tashin gwauron zabi.

Sai dai kuma Bankin ba ya tunanin matsalar za ta tsananta kamar shekarun baya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.