BBC navigation

'Yan tawayen Syria sun shiga cikin Aleppo

An sabunta: 25 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:26 GMT

Garin Aleppo da yaƙi ya ɗaiɗaita

Rahotannin dake fitowa daga birnin Aleppo na Syria na cewa mayaƙan 'yan tawaye sun kutsa kai cikin yankunan Kiristoci dake kusa da birnin.

Wata majiyar masu fafutuka a lardin Asharafiyeh a Aleppon ta faɗawa BBC cewar, 'yan tawayen ga alamu sun karɓe ikon unguwannin sabuwar Seryan da kuma tsohuwar Seryan.

Cigaban da aka samu a baya bayannan nan a Aleppon, na zuwa ne yayin da ake cigaba da tsammanin cewa gwamnatin Syria mai yiwuwa ta sanar da cewa ta amince da yarjejeneiyar tsagaita wuta ta kwanaki hudu, wacce zata soma aiki da zarar an tafi hutun bukukuwan Sallah daga gobe

Wakilin ƙasa da ƙasa a Syrian Lakhdar Brahimi, ya bayyana shirin tsagaita wutar a matsayin wani ɗan ƙaramin mataki da ka iya bada damar gudanar da ayyukan jin kai, da kuma haifar da wata kafa ta tattaunawa a Syria.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.