BBC navigation

Mahaukaciyar guguwa na kara karfi da karatowa Cuba

An sabunta: 25 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:03 GMT
Mahaukaciyar guguwar Sandy a kasar Jamaica

Mahaukaciyar guguwar Sandy a kasar Jamaica

Mahaukaciyar guguwar nan da aka yiwa lakabi da Sandy ta ratsa kasar Jamaica, inda ta kara karfi zuwa kasar Cuba.

Wani gidan talabijin na kasar ya ce kusan kashi saba'in bisa dari na tsibirin ya kasance babu hasken wutar lantarki, bayan da iska mai karfi da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kayar da bishiyoyi da turakun wutar lantarkin.

Mutum guda ne dai aka bayyana ya rasa ransa.

An dai rufe makarantu da filayen saukar jiragen sama, kana hukumomi sun yanke shawarar hana mazauna yankin zirga-zirga a birane, da kasancewa cikin gidajen su domin kiyaye hadurra da gujewa sace-sace.

Cibiyar lura da afkuwar mahaukaciyar guguwa ta Amurka ta ce ruwan saman zai haifar da ambaliyar ruwa, da zaftarewar tabo, da ka iya yin barazana ga rayuwar jama'a musamman a wurare masu tsaunuka, inda ta kuma yi hasashen cewa mahaukaciyar guguwar ta Sandy zata kai har kasar Haiti.

Wani kwararre a fannin binciken yanayi a kasar Cuba Jose Rubiera ya ce Yanzu haka dai guguwar na kara tunkarar yankin gabashin Cuba, ya kuma kara da cewa hasashe ya nuna cewa za ta ci gaba da matsawa zuwa arewa da arewa maso gabas, tana kara gusowa zuwa yankin gabashi, kana zai yiwu ma ta iso yankin kudanci da yammacin yau tsakanin lardin Granma da Santiago.

Shugaban kungiyar tsaro ta kasar Cuba dai ya ce ya kamata a ce mutane sun kaucewa guguwar tunda sun riga sun baiwa jama'a isasshen lokaci ta hanyar sanar musu da wuri, saboda haka za su iya daukar matakan kare kan su.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

  • ,
  • ,

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.