BBC navigation

Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

An sabunta: 25 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:27 GMT
Fira Ministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu

Fira Ministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu

Gwamnatin Israela da kungiyar Hamas sun ce sun cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Gaza, sakamakon tattaunawar da Masar ta shirya tsakaninsu.

Sai dai izuwa yanzu ba a san sharudda da kuma wa'adin dakatar da bude wutar ba, wadda aka cimma bayan tashe-tashen hankulan da aka yi ta yi wadanda a lokacin Israela ta kashe 'yan gwagwarmayar Hamas akalla shida tun ranar Litinin.

Yayin da ita kuma Israelan ta ce Hamas din ta harba manyan makamai da kuma roka-roka sama da 70 zuwa kan iyakarta inda suka raunata mutane 5, uku daga cikinsu munanan raunuka.

Wata majiya daga Hamas ta ce kungiyar ba ta son ci gaba da gwabza fadan, yayin da iyalai ke kai komon shirye-shiryen hutun bukukuwan babbar Sallah a cikin karshen makon nan.

A baya dai Fira Ministan Israela Benjamin Netanyahu ya yi alwashin ci gaba kai hare-hare kan 'yan tada kayar baya dake kaddamar da hare-haren rokoki kan kasar Isra'ila.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

  • ,

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.