BBC navigation

Ƙarancin mai ya tsananta a Lagos

An sabunta: 25 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:44 GMT

Yankin Niger-Delta mai arziƙin mai

A Najeriya yanzu haka matsalar karancin man petur ta ƙara tsanani, inda jerin gwanon ababawan hawa dake neman man petur ɗin ke ƙaruwa a gidajen mai dake birnin Lagos.

Da yawa daga gidajen man a yau sun dakatar, ko kuma babu man sayarwa ga masu ababan hawa.

Yanzu haka dai wasu ƙalilan daga gidajen man ke sayar da kowacce litta daya aka naira dari da ashirin.

Tun daga watan Janairu lokacin da gwamnatin Najeriya ta soma janye tallafin mai wasu sassan ƙasar ke fama da ƙarancin mai.

Najeriya dai na daga cikin kasashen dake kan gaba wajen fitar da mai zuwa kasashen waje, amma wasu lokuttan jama'a kan fuskanci karancin mai.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.