BBC navigation

Kungiyar kasashen Afirka ta dagewa kasar Mali takunkumi

An sabunta: 25 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:17 GMT
Sojojin kasar Mali

Sojojin kasar Mali

Kungiyar kasashen Afrika ta AU, ta dage dakatarwar da ta yi wa kasar Mali daga cikinta, matakin da ta dauka akan kasar bayan da sojoji su ka yi juyin mulki a watan Maris.

Wani babban jami'in kungiyar ta AU, Ramtane Lamamra ya ce an dauki wannan mataki ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali na siyasar kasar.

Ya ce a watan Afrilu na shekara mai zuwa za a gudanar da zabe watanni 12 bayan kasar ta dawo kan turbar tsarin mulki.

Tun lokacin juyin mulkin dai 'yan tawaye masu kishin Islama suka mamaye arewacin kasar ta Mali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.