BBC navigation

Gwamnatin Syria ta amince da shirin tsagaita wutar wucin gadi

An sabunta: 25 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:48 GMT
Syria

Za a tsagaita wuta daga ranar juma'a

Gwamnatin Syria ta amince da shirin tsagaita wuta na wucin gadi a rikicin ta da 'yan tawaye wanda zaiyi daidai da bukukuwan babbar Sallah

Gidan talabijin na Syria ya bada sanarwar cewa dakarun Kasar zasu dakatar da kai farmakin soji kama daga safiyar juma'a har zuwa ranar litinin, matukar ba a sami hare haren 'yan tawaye ba.

Wakilin kasa da kasa akan Syrian Lakhdar Brahimi, shine ya gabatar da shirin tsagaita wutar, wanda kuma yace ya samu amincewar akasarin kungiyoyin 'yan tawayen.

Yayinda shirin tsagaita wutar ke karatowa, an ruwaito cewar mayakan 'yan tawaye a Syria sun kutsa kai cikin tsakiyar birnin Aleppo inda nanne ake fafatawa mako da makonni

Shaidu da masu fafutuka sunce dakarun gwamnati sun janye daga lardunan kiristoci biyu, da kuma wata unguwar Kurdawa, inda suka baiwa mayakan 'yan tawayen damar shiga ciki

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.