BBC navigation

Jirgin sama dauke da gwamnan jihar Taraban Najeriya yayi Hadari

An sabunta: 25 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 21:22 GMT
Jirgin Dana

Wani jirgi da ya yi hadari a Najeria

Ma'aikatar lura da harkokin zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya ta bayar da sanarwa hadarin wani jirgin sama dauke da gwamnan jihar Taraba a Yola, Jihar Adamawa.

Jirgin kirar Cessna 208 mai dauke da fasinjoji shida da suka hada da gwamnan Danbaba Suntai ya tashi ne daga garin Jalingo, jihar Taraba kan hanyar sa ta zuwa Yola da yammacin Alhamis ne kafin ya gamu da hadarin.

Bayanai sun ce wadanda hadarin ya rutsa da su sun samu munanan raunuka, kuma an kwashe su zuwa asibiti domin yi musu magani.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.