BBC navigation

An kone unguwar Musulmi kurmus a yammacin Burma

An sabunta: 27 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:44 GMT
Wasu daga cikin mutanen da suka tserewa rikicin Burma

Wasu daga cikin mutanen da suka tserewa rikicin Burma

Kungiyar Kare Hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch mai hedkwata a Amurka ta tattara bayanai a kan abin da ga alama barnar da aka yi ne a daya daga cikin yankunan da rikicin kabilanci ya shafa wannan makon a yammacin kasar Burma.

Hotunan da aka dauka ta tauraron dan-Adam, wadanda kungiyar ta Human Rights Watch ta wallafa, sun nuna barnar da aka yi a tsakanin al'ummun yammacin kasar ta Burma.

Hotunan sun nuna alamun yadda aka kone ilahirin wata unguwa kurmus a garin Kyaukpyu da ke gabar teku.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce akasarin mazauna unguwar Musulmin Rohingya ne, wadanda ke fuskantar hare-hare daga al'ummar Burma wadanda ba Musulmi ba.

Wadanda ba Musulmi ba dai na cewa ne Musulmin ba ’yan kasar ba ne.

Kungiyar ta ce an yi kacakaca da gidaje fiye da dari takwas.

Mazauna sun tsere zuwa cikin teku

Ana kyautata zaton da dama daga cikin mazauna unguwar sun tsere ta kananan jiragen ruwa zuwa cikin teku.

Wadanda ba Musulmi ba sun bayar da rahoton cewa a wannan karon su ma dakarun gwamnati sun yi harbe-harbe a kansu yayin hatsaniyar, kuma mutane da dama daga cikinsu sun jikkata ko sun rasa rayukansu.

Gwamnatin dai ta ayyana dokar hana fita a yankunan da abin ya shafa, sai dai kuma ana ta sukar lamirin matakin da take dauka tun farkon barkewar rikicin a watan Yuni da cewa bai wadatar ba.

Hukumomi sun ce mutane sittin da hudu sun rasa rayukansu a rikicin na wannan makon.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.