BBC navigation

Kotu a Italiya ta yankewa Silvio Berlusconi hukuncin dauri

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:56 GMT
Silvio Berlusconi

Silvio Berlusconi zai yi zaman gidan yari

Wata Kotu a kasar Italiya ta yankewa tsohon Firayim Ministan kasar Silvio Berlusconi hukuncin dauri a gidan kaso, saboda kin biyan haraji.

An yake masa hukunci ne a kan wani kamfani yada labarai mai suna Mediaset wanda Mista Berlusconi ya mallaka da kuma sayen wani filin shirin talabijin na Amurka ta haramtaciyyar hanya.

Bisa wata sabuwar doka ta afuwa da aka kafa a kasar, an rage yawan hukuncin daurin da aka yanke masa daga shekaru hudu zuwa shekara guda.

Tuni dai 'yan kasar Italiyan su ka soma maida tofa albarkacin bakin su game hukuncin.

Shi dai Mista Berlusconi ya ce an sanya siyasa a cikin shari'ar da akai masa.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.