BBC navigation

Yau musulmai a fadin duniya ke gudanar da bukukuwan babbar Sallah

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:23 GMT
Kasuwar dabbobi ta wucin gadi a Najeriya

Kasuwar dabbobi ta wucin gadi a Najeriya

A yau ne musulmai a fadin duniya ke gudanar da babbar sallah tare da yanka dabbobin layya, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar musu.

Ana dai gudanar da bukuuwan babbar sallar ne kwana daya bayan wadanda suka je aikin hajji a kasar Saudia sun yi tsawuyar Arfa.

Baya ga sallar Idi da ake farawa da ita a cikin ayyukan ibada, ana kuma yanka dabbobi daban-daban a matsayin layya, inda mutane kan ci naman sannan su rabawa 'yan uwa da abokan arziki.

Muhimman ayyukan ibada biyu ne dai ake gudanarwa a duk ranar babbar sallah, inda bayan sallar idin akan kuma yi layyar da niyyar kusanci da Allah.

A Najeriya a yayin da aka fara bukukuwan babbar sallar a yau, jami'an tsaro a wasu sassa na kasar sun bada tabbacin daukar matakan tsaro domin ganin an gudanar da bukukuwan lami lafiya.

Ana dai sa ran malaman addinin Islama a fadin duniya da zasu maida hankali wajen gudanar da huduba da addu'oi na samar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.