BBC navigation

Hadarin jirgin sama dauke da gwaman jihar Taraban Najeriya

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:02 GMT
Hadarin jirgin sama a Najeriya

Hadarin jirgin sama a Najeriya

Bayanai na ci gaba da fitowa fili game da hadarin jirgin sama da ya rutsa da gwamnan jihar Taraba dake arewa maso gabashin Nijeriya a ranar Alhamis, yayin da jirgin mallakin gwamnatin jihar ta Taraba ya tashi daga Jalingo babban birnin jihar zuwa Yola babban birnin jihar Adamawa mai makotaka da ita.

Hadarin dai ya faru ne a birnin na Yola yayin da jirgin ke gab da sauka, kuma bayanai na cewa gwamnan na Jihar Taraba, Mista Danbaba Suntai, ne ke tuka jirgin da kansa a lokacin da ya yi hadarin kuma wasu rahotanni na cewa gwamnan ya mutu amma hukumomi sun bayyana cewa rauni ya samu.

Hadarin jirgin saman da ya rutsa da gwamnan na jihar Taraba Danbaba Suntai da wasu mukarrabansa jiya da maraice a birnin na Yola dai ya haifar da bayanai daban-daban inda har wasu ke cewa gwamnan ya mutu lamarin da har ya haifar da lissafi game da fasalin siyasar jihar ta arewa maso gabashin Najeriya.

Sakataren watsa labarai na gwamnan na jihar Taraba, Malam Hassan Mijinya, ya tabbatar wa da BBC cewa ba a samu asarar rayuka ba a hadarin jirgin.

Ita ma dai ma'aikatar sufurin jiragen sama ta Nijeriya ta fitar da wata sanarawa game da hadarin, inda ta ce mutane shida ne cikin jirgin kuma an kwashe su zuwa asibiti domin jinyar raunuka da suka samu, kana sanarwar ta ce dama ana sa ran jirgin samfurin Cessna 208, zai sauka a filin jirgin na Yola ne da misalin karfe biyar da rabi na yammacin jiya, amma sai sadarwa ta katse tsakanin matukinsa da kuma wurin kula da tafiyar jirgi dake filin jirgin saman na Yola.

Malam Aliyu Bamanga, na daya daga cikin wadanda suka ga yadda jirgin ya fadi kuma suka kwashe wadanda hadarin ya rutsa da su ciki har da gwamna Danbaba Suntai, ya shaidawa BBC cewa wadanda hadarin ya rutsa da su na cikin mummunan yanayi da basa iya magana a lokacin da suka zaro su daga cikin jirgin, sun kuma samu munanan raunuka.

Yanzu haka dai ba a san takamaiman halin da gwamnan na jihar Taraba da sauran wadanda hadarin jirgin ya rutsa da su ke ciki ba bayan hadarin, da kuma sanin hakikannin abinda ya haddasa hadarin na jirgin sama.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.