BBC navigation

Kotu ta sami dan Burtaniya da laifin shigo da makamai Najeriya

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:23 GMT
Taswirar Najeriya

An cafke wani mai shigo da makamai cikin Najeriya

Wata kotu a London ta samu wani dan Burtaniya mai dillancin makamai, Gary Hyde da laifin shigar da taragon jirgin ruwa na makamai ta haramtaciyyar hanya zuwa Najeriya.

An shaidawa kotun cewar, makaman wadanda su ka hada da bindigogi dubu 80 da kuma alburusai miliyon talatin da biyu, an dauko su ne daga kasar China, ba tare da samun izinin hukumomi a Burtaniya ba.

Mutumin da aka kama da laifin kuma ya ki bayyana irin ribar miliyoyin dalolin da ya samu a matsayin riba daga sayar da makaman.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.