BBC navigation

Za a tabbatar da tsagaita wuta na wucin gadi a Syria

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:10 GMT
Tsagaita wuta a kasar Syria

Tsagaita wuta a kasar Syria

Ranar juma'a ne za a tabbatar da tsagaita wuta na wucin gadi tsakanin dakarun Syria da mayaka 'yan tawaye, domin bukukuwan babbar sallah.

Gidan Talabijin na kasar ya ce Rundunar Sojin Syriyar za ta dakatar da ayyukanta na sojin daga ranar Jumma'a har zuwa Litinin.

Hukumar Lura da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana cikin shirin ko ta kwana wajen aikewa da kayayyakin agajin gaggawa ga dubun dubatar iyalai.

Babban mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria, Lakhdar Brahimi ne ya bayar da shawara tare da yin kira ga bangarorin biyu da su tsagaita wutar na wucin gadi, inda ya ce akasarin kungiyoyin 'yan tawayen su ma sun amince da daukar matakin.

Sai dai yayinda yake magana a kasar Turkiyya wani memba a majalisar adawar kasar ta Syria, Omar Shawaf ya nuna shakku kan ko shugaba Assad zai amince da batun tsagaita wutar.

Mr Shawaf ya ce a matsayinsu na 'yan adawar kasar Syria, ba su yi amannar cewa Bashar al Assad zai yi biyayya ga wannan shawara ko mataki na tsagaita wuta ba, saboda 'yar manuniya ta nuna tun a yau ma kimanin fararen hula goma sha bakwai ne aka hallaka a Syria cikin sa'oi shida da suka gabata.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.