BBC navigation

An saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:11 GMT
Syria

An ci gaba da kai hare hare a lokutan sallah a Syria

An sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a Syria, tsakanin gwamnati da kungiyoyin 'yan tawaye.

A babban birnin Syrian wato Damascus, wata mota makare da bama-bamai ta kashe akalla mutane biyar da kuma raunata fiye da mutane talatin.

Garin Deraa dake kudancin kasar, bam ya kashe sojoji da dama.

An kuma samu rahotannin artabu a biranen Homs da Hama da kuma lardin Idlib.

Majiyoyin 'yan kare hakkin bil adama sun ce an kashe mutane akalla arbain.

Dukannin bangarorin biyu dai sun zargi juna akan saba yarjejeniyar.

Wakilin kasa da kasa na majalisar dinkin duniyar Lakhdar Brahimi ne dai ya gabatar da shirin tsagaita wutar a lokutan bukukuwan babbar sallah

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.