BBC navigation

Za a fitar da gwamnan Jahar Taraba zuwa Jamus domin yi masa magani

An sabunta: 26 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:01 GMT
Hatsarin jirgi a Najeriya

Wani jirgi dauke da gwamna ya yi hatsari a Najeriya

Ta bayyana cewa dai tuni aka dauki gwamnan jahar Taraba daga Asibitin kwararru na jihar Adamawa dake Yola, inda aka kwantar da shi da wasu mukarrabansa uku bayan da hadarin jirgin sama ya rutsa da su jiya da maraice, domin fita da shi zuwa wani asibiti a kasar Jamus inda za a ci gaba da yi masa magani.

Kakakin gwamnan jihar Taraban, Malam Hassan Mijinyawa, ya tabbatar wa da BBC cewa an dauki gwamnan zuwa Abuja, daga nan kuma jirgi zai dauke shi zuwa kasar Jamus domin jinya.

Dama dai gwamnan Danbaba Suntai, ya samu mummunan rauni , bayan da jirgin da bayanai su ka ce shi ke tukawa ya rikito kasa a gab da lokacin saukar sa jiya da maraice a Yola babban birnin jihar Adamawa

Jirgin dai ya gamu da tangarda ne bayan da sadarwa ta katse tsakanin sa da hasumiyar kula da akalar jirgi dake filin jirgin na Yola.

Sauran wadanda ke tare da gwamnan a cikin jirgin dai sun samu munanan raunuka, akasarinsu a hannuwan su da kafafun su, amma dai kakakin gwamnan jihar Taraban Danbaba Suntai, ya shaida wa BBC cewa gwamnan kadai za a kai kasar ta Jamus domin jinya.

Tun farko dai rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya mutu, abinda har ya haifar da sabon lissafi game da fasalin shugabanci da kuma siyasa a jihar, amma daga bisani hukumomi su ka musanta labarin mutuwar gwamnan, koda yake dai kawo yanzu ba a nuna shi muraran ga jama'ar jihar da ma Najeriya baki daya ba.

Garzayawa da gwamnan zuwa Turai domin neman magani dai, ka iya sake tado da batun rashin ingancin tsarin kiwon lafiya a Najeriya, sakamakon abinda ake ganin sakacin hukumomin kasar ne, inda kuma manyan mutane a kasar ke dogara kan ayyukan kiwon lafiya na kasashen waje, yayin da galibin talakawa 'yan kasar marasa lafiya kuma basu da damar yin hakan.

Haka zalika, rugawa da gwamnan zuwa Kasar Jamus, wata alama ce dake nuni da cewa ya na cikin mawuyacin hali koda yake dai jami'an gwamnatinsa cewa su ke yi akwai alamar sauki ga gwamnan.

Kawo yanzu dai, ba a kai ga tabbatar da musabbabin hadarin jirgin saman ba, inda ma'aikatar sifirin jiragen sama ta Najeriya cikin wata sanarwa tace sai an bincika.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.