BBC navigation

Sigari na kashe mata kamar maza —Bincike

An sabunta: 27 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:33 GMT

matan da suka bar shan sigari suna da shekaru 30 za su yi hasarar wata daya a rayuwar su

Likitoci a Burtaniya sun ce matan da suka bar shan taba sigari yayin da suka kai shekaru talatin za su yi hasarar kimanin wata daya ne kawai na tsawon rayuwar su, amma fa akalla shekaru goma idan har ba su yi watsi da halayyar ba.

Likitocin sun yi nazarin wani bincike ne da aka gudanar na tsawon shekaru goma sha-biyar na fiye da mata miliyan daya wadanda suka fara shan taba a shekarun 1950 zuwa shekarun 1960 lokacin da shan sigarin wani abin yayi ne.

Liktocin sun ce da farko binciken bai gano illar shan sigarin ga mata ba idan an kwatanta su da maza wadanda suka dauki tsawon lokaci suna shan tabar sigari.

Jagoran binciken, Sir Richard Peto na Jam’i’ar Oxford, y ace binciken ya tabbatar da cewa idan mata suka sha sigari kamar yadda maza ke sha, to za su mutu kamar yadda maza ke mutuwa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.