BBC navigation

Berlusconi ya yi fatali da hukuncin kotu

An sabunta: 27 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:49 GMT
Silvio Berlusconi

Silvio Berlusconi zai yi zaman gidan yari

Tsohon Firayim Ministan Italiya, Silvio Berlusconi, ya sa kafa ya shure hukuncin da wata kotu ta yanke masa na daurin shekara guda a gidan yari saboda samunsa da laifin kin biyan haraji, yana mai cewa abu ne da ba zai sabu ba.

Da yake magana a daya daga cikin gidajen talabijin din da ya mallaka, Mista Berlusconi ya bayyana cewa ba a yi masa adalci ba.

A cewarsa ya kasance yana da yakinin cewa za a wanke shi daga tuhumar da ya kira mara kan gado, sannan ya bayyana cewa hukuncin ya daure masa kai.

Hukuncin, a cewar Mista Berlusconi, ya tabbatar da cewa bangaren shari'a na kasar Italiya ya dage yana yi masa bi-ta-da-kulli ba kakkautawa.

'Akwai siyasa a wannan lamari'

Ya kuma kara da cewa ana yin amfani da bangaren na shari'a don cimma wasu muradu na siyasa:

“Ba ko tantama, kamar sauran kararrakin da aka kago don a tuhume ni, wannan hukunci ma na cike da manufofi na siyasa.

“An gurfanar da ni a gaban kotu fiye da sau sittin, alkalan majistare fiye da dubu daya sun gudanar da bincike, sannan an saurari kararraki har sau dubu biyu da dari shida da sittin da shida a shekaru goma takwas da suka gabata”, inji Mista Berlusconi.

Wannan ne dai karo na farko da aka yankewa Mista Berlusconi hukunci saboda samunsa da laifin kumbiya-kumbiya a harkokinsa na kasuwanci.

Tun shekaru da dama da suka wuce aka zargi tsohon Firayim Ministan na Italiya da kaucewa biyan haraji yayin sayen wasu shirye-shiryen talabijin na Amurka don amfanin gidanjen talabijin din da ya mallaka.

Kotun ta umarci Mista Berlusconi ya danka mata wuri na gugar wuri har Euro miliyan goma ba tare da bata lokaci ba.

Sai dai kuma, mai yiwuwa Mista Berlusconi ba zai ko leka gidan jarun ba duk da wannan hukunci saboda wata dokar afuwa da aka kafa a shekarar 2006—da nufin rage cunkoso a gidajen yari—wadda ta tanadi cewa sai kotunan daukaka kara guda biyu sun tabbatar da hukunci kafin a aiwatar da shi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.