BBC navigation

Sojoji sun cafke mutumin da ake zargi da shirya juyin mulki a Guinea Bissau

An sabunta: 27 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 17:45 GMT
Soji a Guinea Bissau

An cafke wanda ake zargi da shirya juyin mulki

Rahotanni sun ambato sojojin kasar Guinea Bissau na cewa dakarun kasar sun cafke mutumin da ake zargin shine ya jagoranci juyin mulkin da aka bankado a makon da ya gabata.

Rahotannin sun ambaci wanda ake zargin Keptin Pansau N'Tchama, wanda aka ce ya komo daga kasar Portugal tun da farkon wannan watan, inda a nan ne yake samun horon soji.

Gwamnatin rikon kwaryar kasar tace harin da aka kai kan barikokin sojin a ranar lahadin da ta gabata na samun goyan bayan kasar Portugal, kasar da tai ma ta mulkin mallaka da kuma hanbararren Fira Ministan Kasar Carlos Gomes Junior.

An dai hallaka mutane bakwai a farmakin da aka kai a wajen babban birnin Kasar na Bissau.

Majalisar sojin Kasar ce ta kirkiri gwamnatin rikon kwaryar kasar wacce ta hanbarar da gwamnatin Mr. Gomes Junior a watan Afrilu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.