BBC navigation

Za a maido da ma'aikatan hakar ma'adinin Platinum bakin aiki a Afirka ta Kudu

An sabunta: 27 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 14:37 GMT
Ma'aikatan ma'adinai a Afirka ta Kudu

Kamfanin Anglo American na shirin dawo da ma'aikatan sa

Kungiyar ma'aikatan hakar ma'adinai mai karfin fada aji ta Afirka ta Kudu tace kamfanin ya amince ya dawo da ma'aikatan da ya kora makonni uku da suka gabata idan har su ka koma aiki zuwa ranar talata.

Kamfanin Anglo American yace zai yiwa ma'aikatan tayin wasu dala dari biyu domin share hanyar dawowar ma'aikatan

Kasar Afirka ta kudun dai tace yaje yajen aiki a bangaren mahakar ma'adinin Platinun da na kwal sun janyowa kasar asarar fiye da dala biliyan guda.

Kuma mutane da dama sun rasa rayukansu a tashe tashen hankulan da suka biyo bayan yaje yajen aikin

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.