BBC navigation

Ana bukatar kai agajin gaggawa a yammacin Burma

An sabunta: 28 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:46 GMT
Musulmi a Burma

Ana bukatar kai doki ga wadanda rikicin yammacin Burma ya shafa

Majalisar dinkin duniya tace ana bukatar ayyukan jin kai cikin gaggawa a Burma ga dubun dubatar mutanen da rikici ya rusta da su a tashe tashen hankulan da su ka auku a jahar Rakhine a yammacin Kasar

Jami'in ayyukan agaji na majalisar dinkin duniyar a Burma Hans Ten Feld ya fadawa BBC cewa wadanda su ka tserewa rikicin na bukatar taimako

Yace abinda ya kamata a samar masu cikin gaggawa shine abinci da kuma muhalli da ruwa da sha'anin kuma kiwon lafiya

To sai dai wani mai magana da yawun Shugaban Kasar ta Burma Zaw Htay ya fadawa Sashen Burma na BBC cewa gwamnatin kasar bata da karin bayanai game da sabbin hare haren da aka kai a yankin, ya kuma ce gwanati a yanzu haka ta inganta sha'anin samar da tsaro a wannnan yanki

Wannan wani rikici ne dai tsakanin musulmi 'yan kabilar Rohinja da kuma mabiya addinin Bhudda

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.