BBC navigation

Wani dan kunar bakin wake ya hallaka akalla mutane takwas a Kaduna

An sabunta: 28 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 13:35 GMT
Harin bom a Najeriya

An kaiwa majami'a hari a Kaduna da safiyar yau

A Najeriya akalla mutune takwas ne su ka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata yayin da wani dan kunar bakin wake ya kai hari akan wani coci a unguwar Yero dake birnin Kaduna.

Dan kunar bakin waken dai ya aukawa cocin ne cikin wata mota kirar marsandi da wuraren karfe 9:30 na safe a lokacin da ake gudanar da addu'oi a cocin.

Har yanzu dai ana ci gaba da garzayawa da wadanda bam din ya rutsa da su zuwa asibitoci daban daban.

Wakilin BBC a Kaduna ya ce ya shiga dakin ajjiye gawawwakin mutane na asibitin Barau Dikko, daya daga cikin asibitocin da aka garzaya da wadanda harin ya rutsa da su, inda yace ya ga gawawwakin mutane akalla guda hudu wadanda harin ya rutsa da su. Ya kuma ce akalla mutane sittin ne su ka jikkata.

A yanzu haka dai jama'a da dama a Kadunan sun koma cikin gidajen su yayin da aka shiga cikin zaman zulumi

Tuni dai aka baza jami'an tsaro a garin na Kaduna, wanda ya sha fama da fadan da ake dangantawa da addini.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.