BBC navigation

Harin Al Shabab ya yi sanadiyyar kisan wani babban komandan sojin Somalia

An sabunta: 28 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:06 GMT
Mayakan Al Shabab a Somalia

An hallaka babban Komandan sojin Somalia

An kashe wani babban kwamandan sojan gwamnatin Somalia yayin wani harin sari ka noke da 'yan kungiyar Al Shabaab su ka kai.

Gwamnan lardin Shabelle dake kudancin Somalia, yace, an kashe Janar Ibrahim Muhammed Farah Gordon da wasu soja uku ne a kusa da garin Merca dake gabar teku.

Kungiyar Al Shabab wacce ke rike da iko da mafi yawancin yankunan kudanci da kuma tsakiyar Somalia, kwanan nan sun janye daga wasu manyan garuruwa da su ka hada da garin na Merca.

Kungiyar ta Al Shabaab dai ta na ci gaba da kai hare-haren sari ka noke.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.