BBC navigation

Gloria Aroyyo ta gurfana a gaban kuliya

An sabunta: 29 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 06:50 GMT

Gloria Aroyyo

Tsohuwar shugabar kasar Phillipines, Gloria Arroyo, ta gurfana a gaban kuliya domin sauraren tuhumar da ake yi mata ta kashe kimanin dala miliyan tara na kudin cacar lottery a lokacin da take mulki.

Misis Arroyo ba ta nemi afuwa ba, amma alkalin kotun ya rubuta cewa hakan na nufin ba ta aikata laifin ba.

Wannan ita ce kara ta uku ta zargin almubazzaranci da tsohuwar shugabar kasar ke fuskanta.

Da ma dai ana tuhumarta da laifin taimakawa wajen yin magudin zabe, da karbar na-goro a wata huldar kasuwanci da ta shafi kafar sadarwar kasar.

Misis Arroyo tana zargin mutumin da ya gaje ta, watau shugaba Aquino, da yunkurin cin zarafinta duk kuwa da kasancewa tana fama da ciwon wuya.

Sai dai shugaban ya dage cewa dole ne tsohuwar shugabar ta fuskanci hukunci a kan laifukan da ta aikata, yana mai cewa tana kambama batun rashin lafiyarta ne domin jan hankalin duniya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.