BBC navigation

Mutane miliyan 60 a Amurka na shirin fuskantar mahaukaciyar guguwa

An sabunta: 28 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 18:51 GMT
Guguwar Amurka

Mutane miliyan sittin na shirin bala'in guguwar iska

Fiye da mutane miliyan sittin dake zaune a gabashin Amurka dake gabar teku na kintsawa isowar mahaukaciyar guguwar nan mai tafe da ruwa da aka yiwa lakabin 'Sandy' wacce ita ce mahaukaciyar guguwa mai karfin gaske da take barazana ga yankin gabashin Amurka dake gabar teku.

Jami'an gwamnatin gabashin gabar tekun Amurka na bukatar magidanta da su dauki wannan guguwa da mahimmancin gaske.

Magajin garin New york Michael Bloomberg ya bada umarnin kwashe mutane daga yankunan saboda hatsarin ambaliyar ruwa daga guguwar wacce ke karuwa.

Ya dai bada umarnin rufe dukkanin makarantun gwamnati a ranar litinin, kuma yace za a kwashe mutane kusan dubu dari uku da saba'in da biyar wadanda ke rayuwa a wadannan yankuna.

Tuni dai Shugaban Amurkan Barak Obama ya tuntubi manyan jami'an ayyukan gaggawa na Kasar dangane da wannan al'amari, a yayinda Amurkan ke shirin fuskantar daya daga cikin guguwa mafi girma da za ta afkwa yankin cikin shekara da shekaru.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.