BBC navigation

Mali: Hillary Clinton tana ziyara a Algeria

An sabunta: 29 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:03 GMT

Hillary Clinton, sakatariyar hulda da kasashen wajen Amurka

Sakatariyar hulɗa da kasashen waje ta Amurka, Hillary Clinton, tana ziyara yanzu haka a Algeria, domin tattauna shirin da ake yi na aikawa da sojin kasashen yammacin Afrika zuwa Mali, don kokarin kwato arewacin kasar da masu kaifin kishin Islama suka kwace.

Ana dai ganin samun goyon bayan Algeria yana da muhimmanci sosai wajen samun nasarar duk wani yunkurin soja a Mali.

Yanzu haka dai masu kaifin kishin Islama ne ke riƙe da iko da mafi yawan yankin arewacin Mali.

Faransa da sauran kasashen yamma dai suna goyon bayan aike dakarun kasashen waje domin fatattakar masu kishin Islaman na arewacin Mali.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.