BBC navigation

An daure mai fatauncin yaran Najeriya

An sabunta: 29 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 21:21 GMT

Wata kotu dake kudu maso gabashin Ingila ta yankewa wani mutum hukuncin daurin shekaru 20 bisa laifin fataucin kananan yara daga Najeriya zuwa Burtaniya, sannan kuma ya sayar da su ga kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka, wadanda ke tilasta masu yin karuwanci.

Kotun ta ce mutumen, mai suna Osezua Osolase, yana yaudarar yara ne marayu marassa galihu inda ya ke yi masu alkawarin cewa zai kai su Burtaniya don kyautata rayuwarsu.

Yana amfani da tsubbu wajen razana yaran domin su bada kai.

Kotun dai ta same shi da laifukan da suka hada harda fataucin mutane da yin lalata da kananan yara da kuma fyade.

Alkalin da ya yi mashi shari'a ya ce Osolase ba shi da imani da tausayi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.