BBC navigation

Mahaukaciyar guguwa ta tunkaro Amurka

An sabunta: 29 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:38 GMT

Masu bincike da hasashen yanayi a Amurka sun yi gargaɗin cewa mahaukaciyar guguwar nan haɗi da ruwan sama da ake yiwa laƙabi da Sandy, tana yin barazana ga ga mutane kimanin miliyan hamsin.

Yanzu haka dai mahaukaciyar guguwar ta Sandy ta doshi gabar ruwan gabashin Amurka inda dimbin jamaa ke zaune.

Ana sa ran a sakamakon mahaukaciyar guguwar, yankunan dake cikin kwari a birnin New York za su yi fama da ambaliyar ruwa, abun da ya sa mahukunta suka umarci mutane kusan dubu dari huɗu da su fice daga gidajensu.

Yanzu haka dai an rufe makarantu a birnin na New York, kuma harkokin sufuri sun tsaya cik.

Wannan lamari dai yasa 'yan takarar zaben shugaban kasar sun sanar da dakatar yaƙin neman zaɓe.y

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.