BBC navigation

Mutane 20 sun rasu a hadarin mota a kan hanyar Jos zuwa Bauchi

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:44 GMT
mjota

Ana yawan samun haduran motoci a Najeriya

A Jihar Bauchi dake arewacin Nijeriya, hukumomi sun yi karin haske kan wani mummunan hadarin mota da ya faru tsakanin Jos babban birnin Jihar Filato da kuma birnin Bauchi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane ashirin.

Hadarin dai ya faru ne jiya da almuru, inda tara daga cikin wadanda suka gamu da ajalinsu suka kone kurmus nan take.

Daga cikin mutanen da hadarin ya rutsa da su, har da wasu yara takwas 'yan gida daya kuma a kokarin mahaifinsu na zuwa inda lamarin ya auku, sai ya gamu da 'yan fashi amma babu abinda ya same shi.

Kakakin hukumar kiyaye haduran hanya ta Nijeriya a jihar ta Bauchi, Malam Ibrahim Gaidam, ya shaidawa BBC cewa motoci uku ne hadarin ya rutsa da su, tsakanin wata motar safa da fito daga Jos da kuma wata mota kirar 'Station Wagon' samfurin Passat da ta fito daga ta Bauchi, suka yi taho-mu-gama, kana wata motar kirar 'Peugeout' ita ma ta rufta cikinsu.

A cewar kakakin na hukumar kiyaye haduran hanya, gobara ta tashi nan take da motocin suka yi karo, kuma daga cikin mutane ashirin da motocin ke dauke da su, mutane tara sun kone kurmus suka mutu, inda wasunsu ba a ma iya shaida ko maza ko kuma mata ne , yayin da wasu hudu kuma suka samu raunuka amma sauran bakwan suka tsira da lafiyarsa.

Hadura a hanyoyin mota dai a cewar masana na daga cikin abubuwa da suka fi haddasa hasarar rayuka da jikkatar mutane a Nijeriya.

Galibi ana dora laifin ne a kan rashin kyauwun hanyoyin mota da lafta kayayyaki ko fasinjoji fiye da kima, da rashin cikakkiyar lafiyar ababan hawan, da tukin ganganci da kuma yin karan tsaye ga dokokin hanya baki daya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.