BBC navigation

An kashe dan jarida yana karanta labarai

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:33 GMT

Taswirar Bolivia

A kasar Bolivia wadansu mutanen da ba a shaida su ba sun kai hari a kan wani ma'aikacin gidan radiyo a daidai lokacin da yake gabatar da wani shiri.

Ma'aikatan wani sanannen gidan radiyo a kudancin kasar sun ce wadansu mutane ne su hudu, wadanda suka rufe fuskokinsu, suka kutsa kai cikin dakin watsa shirye-shiryen, suka kwarawa Fernando Vidan fetur, suka cinna masa wuta.

An garzaya da Mista Vidal da wani ma'aikaci asibiti inda ake yi musu magani a dakin duba marasa lafiya masu bukatar kulawa ta musamman.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.