BBC navigation

Majalisar dokokin Libya ta amince da sababbin Ministoci

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:27 GMT
Ali Zeidan, Pirayim Ministan Libya

Ali Zeidan, Pirayim Ministan Libya

Majalisar dokokin Libya ta amince da sabuwar majalisar Ministocin da Pirayim Minista, Ali Zeidan, ya gabatar, bayan makunni na sa -in- sar siyasar da ta janyo korar magabacinsa.

An dai takaita zaman majalisar, yayinda dakarun tsaro suka yi harbi a sama domin tarwatsa masu zanga zanga a wajen ginin.

Wakiliyar BBC ta ce mutane da yawa na daukar sabuwar majalisar ministocin a matsayin wani babban kawance, da ya hada masu sassaucin ra'ayi da masu kishin Islama da kuma 'Yan Indipenda.

Sababbin Ministocin sun hada da mata biyu.

An yi watsi da wani kokari na samun yardar majalisar dokoki a ranar talata bayan da sau biyu masu zanga zanga suna kawo cikas ga taron.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.