BBC navigation

Kamfanin Sirius Energy na Najeriya ya samu kwangilar hakar mai a Nijar

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 16:27 GMT
Masu zanga zangar kudin Mai a Nijar

Masu zanga zangar kudin Mai a Nijar

A jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta ba kamfanin Sirius Energy Resources Ltd na Najeriya lasisin gudanar da binciken man fetur a
kasar .

A jiya ne dai aka cimma yarjejeniyar.

A karkashin yarjejeniyar kamfanin na Sirius Energy Resources Ltd, ya amince ya zuba wa kasar ta Nijar Dola miliyan 5.

Kudin za su kasance a matsayin kudin lasisin bincike tare da aiwatar da wasu ayyukan kyautata jin dadin rayuwar jama'ar yankin da ake aikin binciken a cikinsa.

Kamfanin na Najeriya dai na daga cikin wasu kamfanoni 5 ne na duniya da kowane ya ajiye takararsa ta neman lasisin.

Babban Sakatare a ma'aikatar Makamashi da albarkatun man Fetur na Nijar, Gaya Mahamman Lawan ya ce, an baiwa Kamfanin na Najeriya wannan dama dai na daga cikin manufar Gwamnatin ta Jihar ta janyo 'yan kasuwa na kasashe makwabta don taimakawa ga habbaka tattalin arzikin kasar.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.