BBC navigation

An yankewa jagorar 'yan adawar Kasar Rwanda hukuncin zaman gidan yari

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:18 GMT
Ingabire a tsare

Ingabire za ta shafe shekaru 8 a gidan yari

An yankewa jagorar 'yan adawar Kasar Rwanda Victoire Ingabire hukuncin zaman gidan yari na shekaru takwas akan caje cajen aikata ta'addanci da kuma aikata kisan kare dangi data musanta

Kotun ta kuma wanke Mrs. Ingabire, 'yar kabilar Hutu daga wasu caje caje guda biyu

Ta kuma kauracewa zaman sauraron shari'ar.

Ta dai kasance a gidan yari tun watan Oktobar shekarar 2010 bayan a taron tunawa da wadanda akai wa kisan kiyashi, ta bayyana cewa kamata ya yi a tuna wadanda abin ya shafa 'yan Hutu

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta bayyana shari'ar da cewar an sanya siyasa a cikinta

Lawyanta kuma yace zasu daukaka kara

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.