BBC navigation

Har yanzu akwai wariyar launin fata a Afurka ta Kudu

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 15:41 GMT
Masu zanga zanga a  Afirka ta Kudu

Masu zanga zanga a Afirka ta Kudu

An bayyana sakamakon kidayar jama'ar da aka gudanar a Afirka ta Kudu, inda sakamakon ya nuna cewa yawan al'ummar kasar ya karu da mutum miliyan bakwai a shekaru goman da suka gabata.

A yanzu haka dai kasar tana da kusan mutum miliyan hamsin da biyu, amma duk da kawo karshen zamanin wariyar launin fata, har yanzu kasar a rabe take, dangane da abinda ya shafi launin fata

Kudaden shiga da Iyalai bakaken fata 'yan Afirka ke samu ya karu sosai fiye da kowacce kungiya a Kasar, amma iyalai fararen fata na samun ninkin abinda bakake ke samu har sau shida.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.