BBC navigation

An kashe Janar Abdullah Mahmud al Khalidi a birnin Damascus

An sabunta: 30 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 19:09 GMT
Sojojin 'yan tawaye a Syria

An harbe wani janar a rundunar sojin saman Syria

Gidan talabijin na Syria yace dakarun 'yan tawaye sun kashe wani janar na sojin sama mai suna Abdullah Mahmud al Khalidi a birnin Damascus

Rahotan yace Janar Khalidi ya taba kasancewa daya daga cikin kwararru a bangaren harkokin jiragen sama a Syria

Rundunar 'yan tawayen Kasar Syrian dai ta ce ita ta kaddamar da harin.

Sai dai rahotannin da ba a tabbatar da su ba, na nuni da cewar an kashe Janar din ne da yammacin ranar litinin

An sami Labarin kisan a yau, yayinda jiragen sojin saman Kasar da kuma helicoptocin yaki suka inganta hare haren su akan wuraren da 'yan tawaye suke a daukacin Kasar

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.