BBC navigation

An cafke wani mai safarar kwaya a Argentina

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 08:20 GMT

'Yan sanda a Argentina

'Yan sanda a kasar Argentina sun ce sun cafke wani babban mai safarar miyagun kwayoyi dan asalin kasar Colombia.

An kama Henry de Jesus Lopez ne wanda aka fi sani da suna Mi Sangre, ko kuma Jini na a wani gidan cin abinci a babban birnin kasar ta Argentina wato Buenos Aires, inda yan sanda su ka ce ya tsere don gudun kada a kama shi.

Henry, shi ne jagoran gungun nan da ake kira Urabenos wadda ke jagorancin yawancin safarar miyagun kwayoyi a arewacin kasar Colombia.

Shugaban kasar Colombian Juan Manuel Santos ya daura damarar yaki da kungiyoyin safarar miyagun kwayoyi kamar Urabenos.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.