BBC navigation

Ayaba za ta zama abinci ga miliyoyin mutane-Bincike

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:29 GMT

Majalisar Dinkin Duniya

Wadansu masu bincike dake yi wa Majalisar Dinki Duniya aiki sun ce ayaba za ta kasance daya daga cikin muhimman kayan abinci ga miliyoyin mutane, sakamakon matsalar dumamar yanayi.

Rahoton wani bincike da kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan samar da abinci ya dauki nauyin gudanarwa ya yi hasashen cewa kayayyakin abinci kamar masara, da shinkafa, da alkama, za su ragu a kasashe masu tasowa da dama.

A kasashe masu sanyi kuma, dankali zai ragu saboda dumamar yanayin.

Rahoton ya kuma yi hasashen cewa, a wasu kasashen, ayaba za ta kasance zabi mafi sauki ga mutane da dama.

Sauran kayan abinci kuma da za su maye gurbin wadanda aka fi amfani da su su ne rogo a madadin alkama a kasashen dake kudancin Asiya, sannan jan wake ya maye gurbin waken soya a kasashen Afirka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.