BBC navigation

Guguwa: Obama ya ziyarci New Jersey

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 20:05 GMT
obama

Barack Obama ya ziyarci yankunan da guguwa ta yiwa barna

Shugaba Obama ya ziyarci New Jersey domin gane wa idanunsa irin barnar da gawurtacciyar mahaukaciyar guguwar da ta yi kaca - kaca da yankin arewa maso gabacin Amurkar ta haddasa.

Mista Obama ya jingine yakin neman zaben Shugaban kasa domin mayar da hankali a kan mahaukaciyar guguwar, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 50 a jihohi tara.

An bude biyu daga cikin filayen jiragen saman birnin New York yayindahukumomi a arewa maso gabacin Amurka ke aiki domin maido da muhimman ababen more rayuwar jama'a bayan barnar da guguwa dake tare da ruwa ta haddasa.

Jiragen sama sun sauka a filayen jirage na JFK da kuma Newark, filayen da suka fi hada hada a kasar.

Bas - bas da kananan jiragen kasa na jigilar cikin gari da kuma jiragen ruwar sufuri tsakanin unguni sun koma aiki, to amma har yanzu jiragen karkashin kasa na birnin sun ci daga ba zama a rufe,saboda ruwan da ya kwarara cikin hanyoyin ya sa za a ci gaba da rufe su har wasu yan kwanaki masu zuwa.

Sai dai har yanzu gidaje da dama ba su da wutar lantarki, kuma za a cigaba da rufe hanyoyin jiragen kasa na karkashin kasa na birnin na New York.

Fiye da mutane arba'in ne suka rasa rayukan su a laokacin guguwar, kuma sha takwas daga cikin su mazauna birnin New York ne.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.