BBC navigation

An kashe dan kungiyar Musulmi a Tunisiya

An sabunta: 31 ga Oktoba, 2012 - An wallafa a 07:40 GMT

Shugaban kasar Tunisiya, Mancef Marzouki

Mahukunta a kasar Tunisia sun ce an kashe wani mayakin kungiyar Musulmi ta Salafi, a lokacin da suka kai wani hari kan wani caji ofis dake babban birnin kasar Tunis.

Wani mazaunin birnin ya ce jami'an tsaro sun yi amfani da albarusai da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa mutanen da suka kai harin.

Wadanda suka kai harin suna nuna fushinsu ne kan kama wani dan kungiyar ta Salafi, wanda ake zargi da cakawa wani dan sanda wuka a ranar Asabar din da ta gabata.

'Yan sanda biyu ne suka jikkata sakamakon harin na ranar Talata.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.