BBC navigation

Ana yajin aiki a wasu kasashen Turai

An sabunta: 14 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:23 GMT
Zanga zanga a Portugal

Zanga zanga a Portugal

Jama'a a kasashen Spain da Portugal na gudanar da zanga zanga a matsayin wani bangare na nuna kin amincewa da matakan tsuke bakin aljihu da ake a duk fadin Turai.

Harkokin zirga zirga da kasuwanci sun tsaya cik, yayin da su ma makarantu suka rufe a dukkan kashen biyu.

Haka nan kuma an samu hatsaniya a birane da dama na kasar Spain.

An jikkata 'yan sanda 6 a Italiya, yayin da masu zanga zanga suka yi arangama da 'yan sandan kwantar da tarzoma a Turin da Milan.

Haka nan kuma an yi kiran da a tafi yajin aiki a wasu kasashen Turai 20 da suka hada da Girka, da Faransa da Jamus da kuma Poland.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.