BBC navigation

An gurfanar da Dan Jaridar Girka kan tona asirin wasu gaggan 'yan kasar

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:33 GMT
Editan Kostas Vaxevanis

Editan Kostas Vaxevanis

A birnin Athens an soma shari'ar wani Editan wata Mujallar kasar Girka da ya wallafa jerin sunayen wadanda suke kin biyan haraji.

Editan, Editan Kostas Vaxevanis, ana tuhumarsa da keta yancin sirri ta hanyar buga sunayen Yan kasar ta Girka dubu 2 dake da asusun ajiya a Bankunan kasar Switzerland.

Sun hada da hamshakan yan kasuwa da lauyoyi da yan jarida da kuma wani tsohon Minista.

An mika sunayen ga gwamnatin Girka, to amma ta ki ta bincike su.

Mr Vaxevanis ya ce kamata yayi a gurfanar da yansiyasar da suka ki daukar matakai.

Sai dai dan jaridar ya ce bai wallafa bayanann sirrin mutane ba,domin bai bayyana adadin kudaden da suka boye a asusun bankin ba.

A binda ya wallafa kawai shi ne sunaye da kuma bankunan da suke a jiye a ciki.

Wannan abu ne da kowa ya sa ni, ba wanda yake badda kama idan za shi banki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.