BBC navigation

Matasa sun yi wata zanga zanga a Jos

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:04 GMT
Masu zanga zanga a Najeriya

Masu zanga zanga a Najeriya

Matasa masu yawan gaske a Jos babban birnin Jihar Pilato sun fita kan titunan birnin don wata zanga-zangar nuna rashin jin dadi da abin da suka kira mawuyacin hali da yajin aikin ma'aikatan kananan hukumomi ya jefa jihar ciki.

Hukumomi dai sun yi yunkurin hana zanga-zangar domin gudun tashin hankali a birnin, amma daga bisani suka kyale su, jami'an tsaro kuma suka yi masu rakiya. An kuma kammala zanga-zangar cikin lumana.

Dimbin matasan na jihar Filato karkashin inuwar babban Zauren Kungiyar Matasan Jihar Filato, sun fito ne suka karade tituna da dama a jos babban birnin jihar.

Suna kuma dauke da kwalaye masu rubuce - rubucen da ke yin tir da kuma Allah Wadai da gwmnatin jihar ta Filato kan abin da suka kira rashin biyan ma'aikatan kananan hukumomi hakkinsu.

To sai dai kuma gwamnatin jihar Filaton ta bakin Kwamishinanta na watsa labarai ta ce hayar matasan ne aka yi .

Kungiyoyin kwadago a jihar Filaton dai sun sha musanta zargin cewa akwai wadanda ke zuga su ci gaba da yajin aikin domin bakanta gwamnati.

Haka nan kuma su ma matasa masu zanga-zangar sun musanta zargin cewa an saye su domin su yi zanga-zangar ne.

Yanzu haka dai an kasa cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin jihar Filato da ma'aikatan kananan hukumomi da suka yi watanni shidda kawo yanzu suna yajin aiki kan batun sabon tsarin albashi mafi kanknata na naira dubu goma sha takwas.

Babban batun da ake takaddama a kai yanzu shi ne matsayin gawmnati na cewa ba za ta biya ma'aikatan albashin lokacin da ma'aikatan ke yajin aiki ba, su kuma ma'akatan na cewa lallai sai ta biya su.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.