BBC navigation

An tuna da mutanen da suka rasa rai a Jos

An sabunta: 28 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:28 GMT
Taswirar dake nunin garin Jos

Taswirar dake nunin garin Jos

Al'umar Hausawa na Jos babban birnin jihar Filato sun gudanar da wani taron addu'o'i don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu bayan mummunan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben kanananan hukumomi a jihar a shekara ta dubu biyu da takwas.

Zaben da aka bayyana cewar jam'iyyar PDP mai mulki ce ta lashe shi.

Mutane kimanin dubu daya ne suka rasa rayukansu a lokacin tashin hankalin wanda ya barke ranar ashirin da takwas ga watan Nuwamba na shekarar.

Kungiyoyin kare hakkin bil-Adama sun bayyana a rahotanni daban-daban cewa jami'an tsaro ne suka aikata akasarin kashe-kashen mutanen, saida jami'an tsaron sun musanta rahotannin.

Haka kuma suma Kiristoci sun rasa rayuka a tashin hankalin, sun kuma yi watsi da rahotannin kungiyoyin kare hakkin Bil Adamar.

An dai yi kiyasin cewar an nyi asarar dukiyar da kudinta za su kai fiye da Naira Biliyan 20.

Jihar ta Filato dai ta dade tana fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.