BBC navigation

Mutane da yawa sun mutu a wani artabu a arewacin Mali

An sabunta: 20 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:16 GMT
'Yan tawayen arewacin Mali

'Yan tawayen arewacin Mali

Jami'ai a kasar Mali sun ce an kashe mutane da dama a arangama tsakanin mayaka 'yan kishin Islama da na azibinawa yan tawaye a arewacin kasar.

Rahotanni na cewa an gwabza fadan ne a 'yan kwanakin da suka wuce, a kewayen garin Menaka, dake yankin Gao.

Wani jami'i a garin na Menaka, wanda a da yake hannun Azibinawan, ya ce 'yan kishin Islamar sun kai farmaki a garin.

Kasashen Afrika ta yamma, na kokarin kammala shirye shirye na tura sojoji domin shiga tsakani a arewacin Mali, wanda Azbinawa 'yan tawaye da 'yan kishin Islamar suka kwace bayan wani juyin mulki a watan Maris.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.