BBC navigation

Majalisar Nijar ta yi watsi da dokar hakkin 'yan mata

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:18 GMT
Shugaba Mahamadou Issoufou

Shugaba Mahamadou Issoufou

Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da wata dokar kare hakkin 'yan mata.

Majalisar ta ce dokar ta kunshi wasu matakai da ake jin sun saba wa addinin musulunci da kuma al'adu.

Haka nan kuma ta bukaci da a mayar wa gwamnatin da dokar har sai ta yi mata gyaran fuskar da ta dace .

Daga cikin matakan da dokar ta tanadar dai har da batun hana iyaye aurar da 'ya'yansu mata idan suna makarantar sakandare.

Kungiyoyin addinin musulunci dai sun yi Allah wadai da kudurin dokar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.