BBC navigation

Kungiyoyin farar hula a Nijar sun koka da matsayin kasashe kan rikicin Mali

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:29 GMT
Mayakan Kungiyar Islama ta mujao a Mali

Mayakan Kungiyar Islama ta mujao a Mali

Kungiyoyin farar hula a Jamhuriyar Nijar sun soma tofa albarkacin bakinsu a game da kwan-gaba-kwan-baya da sabanin ra'ayin da ake ci gaba da samu tsakanin kasashe a kan shirin amfani da karfi don kwace arewacin Mali daga hannun 'yan tawaye.

Kungiyoyin na ganin tunanin abin da wannan ko waccan kasa ta yammacin duniya za ta samu ne ummul haba'isin cecekucen .

Galibin kasashen suna ganin babu wani arzikin da za su diba take-yanke a kasar ta Mali, musamman idan aka yi la'akari da cewa kasashen yammacin duniyan na fama da matsin tattalin arziki .

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.