BBC navigation

Ma'aikatan Lantarki sun yi zanga zanga a Kaduna

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:28 GMT
Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Ma'aikatan wutar lantarki a Najeriya karkashin wasu kungiyoyi biyu sun gudanar da wani babban gangami a Kaduna domin nuna damuwa a bisa aniyar gwamnati na sayar da kamfanin samar da wutar lantarki na kasar PHCN .

Ma'aikata da dama na wannan kamfani daga shiyyar arewa maso yamma ne dai suka halarci gangamin na Kaduna.

Shugabanin kungiyoyin sun nunawa ma'aikatan bukatar jajircewa a bisa neman hakkokinsu na barin aiki kafin a sayar da kamfanin.

Gwamnatin Najeriya na shirin sayar da Kamfanin samar da wutar lantarki ne dai ga kamfanoni masu zaman kansu .

Wannan wani mataki ne na inganta samar da wutar lantarki a kasar, wani abun da ya jima yana addabar yan kasar da kuma harkokin kasuwanci.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.